14 Nuwamba 2020 - 11:17
An Nada Sabon Shugaban Yankin Tigray A Daidai Lokacin Da Ake Tsoron Rikici Na Kara Kamzamta A Yankin

Majalisar kasar Habasha ta sanar da nada Dr Mulu Nega a matsayin sabon shugaban yankin Tigray na kasar a daidai lokacin da rikicin da ke faruwa a yankin yake kara kazamta da ake zargin ana tafka laifuffukan yaki.

ABNA24 : Firayi ministan kasar Habashan Abiy Ahmed ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinta na Twitter inda ya ce an nada Dr Mulu Nega a matsayin shugaban yankin Tigray.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da dakarun gwamnatin suke ci gaba da kai hare-haren da suka kaddamar a yankin a matsayin mayar da martani ga hare-haren da dakarun yankin na Tigray suka kai wa sansanonin sojojin gwamnatin Tarayyar kasar a kwanakin baya.

A jiya Alhamis ne dai majalisar kasar Habasha ta sanar da cire rigar kariyar da tsohon shugaban yankin na Tigray Debretsion Gebremichael na jam’iyyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF) da aka zaba a watan Satumban da ta gabata, daga baya kuma kafafen watsa labaran gwamnatin kasar suka sanar da cewa an fitar da sammacin kama tsohon shugaba tare da wasu kusoshin jam’iyyar TPLF din saboda laifin barazana ta tsaro da kuma zaman lafiyar kasar.

Rikici dai ya fara kunno kai tsakanin gwamnatin tarayyar da na yankin Tigray din ne bayan da gwamnatin yankin ta yi kunnen uwar shegu da sanarwar jinkirta zaben da gwamnati ta yi, inda ta gudanar da nata zaben da kuma bayyana firayi ministan Abiy Ahmed din a matsayin haramtaccen shugaba.

Rahotanni dai sun ce ya zuwa yanzu dai daruruwan mutane ne suka mutu kana wasu dubbai kuma suka gudu suka bar muhallinsu da tafiya gudun hijira zuwa kasar Sudan sakamakon wannan yaki na kwanaki 10 da ke faruwa tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan tawayen yankin Tigray din.

342/